Bisa labarin da jaridar Al-Shorouk ta kasar Masar ta bayar kan shafinta na yanar gizo ta Internet a ran 1 ga wata da dare na agogon wurin, an ce, babbar kotun gudanarwa ta kasar Masar ta sanar da yin watsi da karar da aka daukaka dangane da maido da tsohon shugaban kasa Muhammed Hosni Mubarak kan mulki, inda kotun ta kuma kara da cewa, wannan shi ne hukunci na karshe, ba za a iya sake daukaka kara kan wannan batu ba.
Kafin wannan kara, wasu lauyoyi uku da wasu magoya bayan Mubarak sun taba daukaka kara a karamar kotun gudanarwa ta Masar don neman a maido da Mubarak kan aikinsa, amma karamar kotun ba ta yarda da wannan bukata ba. (Maryam)