Haka kuma, bangarorin biyu sun tattauna batutuwan yunkurin siyasa a kasar Masar, da halin da ake ciki a kasar Siriya, da maganar samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya da sauransu. Kazalika kuma, Kerry ya yaba wa Shugaba Morsy kan kokarin da ya yi na daidaita rikicin da ke tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas cikin nasara, kuma ya ce, Amurka tana ganin cewa, ba za a iya rasa taimakon kasar Masar ba cikin yunkurin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta tsakiya, ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun tattauna matakan da Amurka za ta dauka wajen taimakawa Masar farfado da tattalin arziki, cikinsu har da ba da kudin agaji da kara fadada yawan kayayyakin da kasar take fitarwa.(Bako)