Shugaba Morsy ya ce, za a canja membobin majalisar ministocin kasar ne don ci gaba da yin kokarin cimma burin da aka tsara a shekarar 2011 lokacin da aka yi zanga-zanga mai tarin yawa a kasar, tare da tabbatar da shigar da fitattun mutane a majalisar ministocin kasar. Kana ya ce, za a canja wasu gwamnonin jihohin kasar.
Shafin internet na Pyramids Online ya tabbatar da wannan labari, amma ya ce, shugaba Morsy bai sanar da ko za a canja firaministan kasar Qandil ba ko kuma a'a.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, shugaba Morsy ya bayyana cewa, za a canja membobin majalisar ministocin kasar bisa bukatun jama'a, ministocin da jama'ar kasar da dama suke goyon baya za su ci gaba da zama mukaminsu, yayin da za a canja wadanda jama'ar kasar ke nunawa rashin goyon baya. (Zainab)