Yayin wannan ziyarar, shugaba Morsy ya nuna cewa, kasar Masar na fatan shiga kungiyar kasashen BRICS, don farfado da tattalin arzikinta.
Yayin taron dandalin tattaunawar harkokin cinikayya tsakanin kasar India da kasar ta Masar da aka yi ran 20 ga wata, shugaba Morsy ya bayyana cewa, a shirin gaggauta farfadowar tattalin arzikin kasar ta Masar, kasarsa na fatan shiga kungiyar kasashen BRICS, ta yadda za ta karfafa hadin gwiwa tsakaninta da kasar India, da dai sauran kasashen dake bunkasa cikin sauri a fannin na tattalin arziki. Har ma ya ambata wani sabon suna da ya kira E-BRICS, wato Egypt da BRICS ke nan, idan har kasar tasa ta samu damar shiga cikin kungiyar.
Morsy ya kuma nuna cewa, bisa gayyatar da aka yi masa, zai halarci taron kolin kasashen BRICS da za a kira a kasar Afirka ta Kudu, a karshen watan Maris. Yana fatan za a ciyar da shirin kafa bankin zuba jari tsakanin kasashe masu tasowa, don ba da taimako ga kasashen wajen inganta ababen more rayuwa ga al'ummunsu cikin sauri. (Maryam)