Jami'yyar adawa ta "the National Salvation Front" ta kasar Masar ta sanar a ran 26 ga wata cewa, ba za ta shiga zaben majalisar wakilai da za a yi a watan Afrilu mai zuwa ba, tana mai sake jaddada kin yarda da halartar shawarwarin al'ummar kasar, karkashin jagorancin shugaba Mohamed Morsy.
Wakilin jam'iyyar kuma shugaban kungiyar lauyoyi ta kasar ne ya sanar da hakan, yayin wani taron manema labaru, yana mai cewa jam'iyyar, ta cimma matsaya daya, dongane da kauracewa da zaben majalisar dokokin dake tafe, tare kuma da kin yarda da halartar shawarwari tsakanin ta da tsagin gwamnatin kasar.
Ban da haka, jagoran 'yan adawar ya nuna cewa, dalilin da ya sa jam'iyya ta ki yarda da zaben shi ne, babu wata shari'a ko tanajin doka, da zai iya tabbatar da adalci da daidaito yayin zaben, kuma gwamnati mai ci ba ta amsa bukatar da suka gabatar mata ba. Rashin halartar jam'iyyar 'yan adawar dai na nuna cewa, a gare su za a yi zaben ne ba bisa ka'ida ba.
Idan dai za a iya tunawa, a ran 23 ga watan nan ne shugaban kasar ta Masar Mohamed Morsy, ya ba da umurnin gudanar da zaben majalisar dokokin kasar, daga ran 22 ga watan Afrilu, inda ake fatan majalisar da za a zaba, za ta gudanar da zama na farko a ranar 2 ga watan Yuni mai zuwa. Jim kadan da bayyana wannan umarni da shugaba Morsy ya yi, sai daya daga shugabannin kungiyar 'yan adawar Mohamed Mustafa ElBaradei, ya sanar da kin yarda da batun shiga zaben, yana mai cewa, zaben da za a yi tamkar damfara ce. Daga baya kuma a ranar 26 ga wata, kungiyar ta sanar da kin yarda da zaben baki daya. (Amina)