in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An dage shari'ar tsohon shugaban kasar Masar zuwa 8 ga watan Yuni
2013-05-12 16:38:14 cri

Wata kotu a kasar Masar ta bayyana dage sabuwar shari'ar da ake yiwa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak zuwa 8 ga watan Yuni mai zuwa.

Wannan mataki yazo ne dai dai lokacin da kotun ke ci gaba da tuhumar Mubarak, da wasu 'ya'yansa biyu, Alaa da Gamal, da kuma tsohon ministan cikin gida zamanin gwamnatin data shude Habib Al-Adli, tare da wasu jami'an tsaro a tsohuwar gwamnatin su 6, da ma wani dan kasuwa mai suna Hussein Salem, da zargin sanya hannu wajen kisan wasu masu zanga-zanga, da kuma wasu karin laifuka masu alaka da cin hanci da rashawa.

A cewar alkalin kotun hukunta manyan laifuka Mahmoud Kamel Al-Rashidi, an dage shari'ar ne domin samun karin lokacin nazartar shaidun da aka gabatar, tare da baiwa masu kare wadanda ake zargi karin lokacin tantance sauran takardun da mai gabatar da kara ya gabatar.

Yayin zaman kotun na ranar Asabar 11 ga watan nan, mai gabatar da kara ya baje kolin laifukan da ake tuhumar Mubarak, da ragowar na hannun damansa da aikatawa, an kuma ce dan kasuwar da yake cikin jerin wadanda ake zargin, wanda kuma tuni ya tsere daga kasar, yana ci gaba da tattaunawa da bangaren mahukuntan kasar, domin duba yiwuwar mika wani kaso mai yawa na dukiyarsa ga gwamnatin, domin kaucewa hukuncin da aka iya yanke masa. Daga karshe kotun ta bukaci da a ci gaba da tsare tsohon shugaba Mubarak da yaransa biyu da tsohon ministan cikin gida, ta kuma bada damar sakin ragowar jami'an tsaron su 6 tsahon dan lokaci.

Don gane da damar da kotun ta baiwa Mubarak na duba yiwuwar amfani da wasu gungun lauyoyin sa kai, yace a mika wannan batu ga lauyansa Farid Al-Deeb, sai dai Al-deeb ya godewa gungun lauyoyin, lokacin da yake bayyana rashin bukatar taimakon nasu.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China