Pereira wanda ya fada wa manema labaru, hakan bayan ganawarsa da shugaban kasar Mozambique Armando Emilio Guebuza ya kara da cewa, hanyar kawai da za a bi wajen cimma burin sake gina kasar Guinea-Bissau ita ce, a yi shawarwari da samun fahimtar juna game da shirya zaben cikin 'yanci da bin tsarin demokuradiyya, a sa'i daya kuma, ya bayyana cewa, yana da imani game da farfado da yanayin da ake ciki a kasar Guinea-Bissau.
A matsayin halataccen shugaban kasar, Raimundo Pereira ya isa birnin Maputo don halartar taron koli na kasashen da suke yin amfani da harshen Português da za a shirya a karshen wannan mako.
A ranar 12 ga watan Afrilu na bana, sojojin Guinea-Bissau suka yi juyin mulki, inda suke hambarar da shugaban wucin gadi Raimundo Pereira, tare da cafke manyan jami'an gwamnati da dama, daga bisani kuma, sakamakon matsin lamba daga kasashen duniya, sojoji da suka yi juyin mulki sun saki wadannan manyan jami'an gwamnatin kasar.(Bako)