Fernando Vaz ya ce, gwamnatin wucin gadin kasar ta riga ta shimfida tsarin sojojin tsaron kasar a yankunan gabas da kudanci, ta yadda za ta iya kiyaye cikakken ikon yankunan kasar yadda ya kamata. Hukumomin sojin kasar dai sun alkawarta bayyanawa al'ummar kasar da ma duniya halin da ake ciki, da zarar an kammala shirin da aka sanya gaba.
Bisa labaran da aka samu daga Guinea-Bissau, sojojin kasar na shirya daukan matakan soja don farfado da matsayin tsohon firaministan kasar Carlos Gomes.
A ranar 12 ga watan Afrilun shekarar bana ne dai, sojojin gwamnatin Guinea-Bissau suka gudanar da wani juyin mulki, inda suka kame wasu manyan jami'an kasar, daga bisani kuma, bisa kiran gamayar kasa da kasa suka amince da sakin firaminista Carlos Gomes, wanda ya yi gudun hijira zuwa kasar Portugal. (Maryam)