Wani jami'in hukumar soja da ke wannan sansanin ya bayyana wa 'yan jarida cewa, harin ya auku ne, wajen karfe 3 na sassafe, inda dakarun suka bude wuta kan sojoji masu gadi, daga bisani sojojin da ke sansanin su maida martani. A halin yanzu dai, wasu daga maharan sun arce, sai dai an aika da wata rundunar soja ta musamman don kamo su.
A ranar 12 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki dai, yayin wani juyin mulki, sojojin kasar ta Guinea-Bissau sun kame wasu manyan jami'an gwamnatin kasar, ciki hadda mukadashin shugaban kasar Raimundo Pereira da tsohon firaministan kasar Carlos Gomes. Haka nan kuma, a cikin watan Mayu, wakilan sojoji masu juyin mulkin kasar, jam'iyyun siyasa daban daban, kungiyar tarayyar kasashen Afirka, da kuma kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka da dai sauran kungiyoyin kasa da kasa, sun kulla yarjejeniyar wucin gadin siyasa a babban birnin kasar Bissau, matakin da zai baiwa kasar shekara guda, wanda bayan kammalar wa'adin ake fatan shirya zaben shugaba kasa da na 'yan majalissar dokokin kasar. (Maryam)