Jami'an sabuwar gwamnatin wucin gadi ta kasar Guinea-Bissau sun kama aiki a ran 23 ga wata a birnin Bissau, babban birnin kasar.
Sabuwar gwamnati da ta kunshi ministoci 14 da sakatarori 13 na harkokin kasar, ciki har da Celestino Carvalho da Musa Diata,sojoji biyu da suka yi juyin mulki, wadanda suka zama ministan tsaro da sakataren gudanarwa na kasar.
Shugaban gwamnatin wucin gadin, Manuel Serifo Nhamadjo ya halarci bikin rantsuwar kama aiki na jami'an sabuwar gwamnati da aka yi a wannan rana, kuma ya yi jawabi cewa, babban nauyin dake bisa wuyan sabuwar gwamnatin kasar shi ne tabbatar da samar da albashi da farfado da makarantu. Ya shawarci sabuwar gwamnati da ta yi gyare-gyare kan harkokin shari'u domin gudanar da zaben shugaba da kafa dokoki cikin adalci da 'yanci. Kuma ya nanata muhimmancin gyare-gyaren da za a yi kan hukumomin tsaro da tsarin harkokin gwamnati.
Kakakin sojojin da suka yi juyin mulki na kasar Guinea-Bissau ya sanar a gun taron manema labaru da aka yi a ran 22 ga wata a birnin Bissau cewa, cibiyar ba da umurni ta sojojin juyin mulki ta mika mulki ga gwamnatin wucin gadi ta kasar a wannan rana.(Lami)