in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akalla fasinjoji 22 sun mutu, wasu 70 sun bace sakamakon nutsewar wani jirgi a Guinea-Bissau
2012-12-29 16:43:35 cri
Akalla fasinjoji 22 sun rasa rayukansu, sauran kimanin 70 sun bace sanadiyyar nutsewar wani jirgin ruwa a kasar Guinea-Bissau a jiya ranar Jumma'a 28 ga wata, kamar yadda ma'aikatan ceto suka bayyana.

Ma'aikatan ceton kasar sun ce, akwai fasinjoji sama da 90 a cikin wannan jirgin da ya yi hadari, ciki har da mutane shida da aka ceto.

An ce, hadarin ya faru ne saboda jirgin ruwan ya dauki mutane fiye da kima, da kuma karfin igiyar ruwa da ya gamu da shi.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China