Kafar yada labaran ta bayar da rahoto a ranar Litinin cewa, jami'an soja da 'yan sanda da ke cikin tawagar sun fito ne daga kasashen Najereiya, Burkina Faso da kuma Senegal, don maye gurbin tawagar Angola da aka tura yau sama da shekara guda zuwa kasar da ta ke magana da harshen Portuguese..
Tawagar ta Angola (MISSANG) wadda ita ma ta ke magana da harshen Portuguese, tana da mambobi 600 ne, kuma ta samu matsala ne da sojojin da suka yi juyin mulki, inda suka cimma wata yarjejeniya a asirce tsakanin tawagar kasar ta Angola da gwamnati karkashin tsohon firaminista Carlos Gomes Junior.
Wata majiyar soja ta bayyana cewa, a karkashin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ECOWAS da sojojin da suka yi juyin mulki, kungiyar za ta kula da tawagar tare da sa-ido kan shirin wucin gadin na shekara daya. A yau ne ake saran sojojin kasar Angola za su fara janyewa daga Bissau.
Kungiyar ECOWAS ta ce, janyewar za ta dauki kwanaki 3 zuwa 4, lokacin da jami'an Angola za su samu kariya.
Ya zuwa yanzu dai an kammala tura tawagogin ECOWAS, inda galibi tun farko aka shirya sanya mata da maza 629 a ciki. (Ibrahim)