Tun dai ranar Talata ce, jingin ruwan kasar Angola mai sunan "Lunda Rio Mbridge", ya loda tankokin yaki guda 8, da motocin silke na yaki guda 8, da tankoki daukar mai guda 4, da kuma motocin shiga daji guda 3, kamar yadda kafar watsa labaran ta sanar.
Kakakin gwamnatin kasar Guinea Bissau, Fernando Vaz ya tabbatar da cewa, wannan shiri na janye sojojin kasar Angola, da ke gudana karkashin sa idon sojojin kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO na tafiya daidai. Har yanzu dai tun da aka fara babu wata matsala da aka fuskanta.
Daga bangaren Kanal Wilson Isaac na tawagar sojin kasar Angola, ya sanar da cewa, janye sojojin na gudana ne tare da dauke kayayyakin sojan.
Sojoji 600 na wannan tawagar sun iso Bissau tun ranar 11 ga watan Maris na shekara ta 2011 bisa yarjejeniyar da aka daddale tsakanin kasashen Guinea Bissau da Angola domin taimakawa kasar Guinea Bissau wajen daidaita lamarin tsaro da kariya.(Abdou Halilou)