Ranar 28 ga wata, kakakin hedkwatar ba da shawara ga rundunar soja ta kasar Guinea Bissau Dahabana, ya shedawa manema labaru cewa, kasar sa, za ta tura sojojointa da yawansu ya kai 140 domin shiga aikin kwato yankin dake arewacin kasar Mali da 'yan tawaye suka mamaye.
Dahabana ya ce, yanzu, wadannan sojoji suna karkashin jagorancin rukunin sojojin kasar Senegal. Ban da wannan aiki, Guinea Bissau ta taba aiwatar da makamancin sa sau da dama Angola, Mozambique, Liberia da sauran kasashe.
A nata bangare kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika wato ECOWAS za ta tura sojojinta 3300 zuwa kasar ta Mali, domin taimakawa wajen dakile tasirin kungiyar 'yan tada-kayar-baya dake arewacin kasar ta Mali. (Amina)