A gun taron manema labaru da aka shirya, kakakin sojojin da suka yi juyin mulki ya ce, dalilin da ya sa sojojin Guinea-Bissau suka yi juyin mulki a ranar 12 ga watan Afrilu, shi ne domin tsohon firaministan kasar Carlos Gomes ya taba yin kira ga sojojin kasashen waje da su kifar da manyan hafsoshin sojojin kasar, don haka sojojin kasar sun yi juyin mulki ne bisa matsin lambar da suka samu.
A watan Maris na bana, Gomes yana kan gaba cikin babban zaben zagaye na farko da aka yi a kasar Guinea-Bissau, kuma ya shiga cikin sunayen 'yan takarar babban zabe a zagaye na biyu da aka nemi gudanar da shi a karshen watan Afrilu. Amma, a ranar 12 ga watan Afrilu, sojojin kasar sun yi juyin mulki, inda suka cafke tare da tsare mukaddashin shugaban kasar Raimundo Pereira da Carlos Gomes da sauran manyan jami'an gwamnatin kasar. A ranar 27 ga watan Afrilu, bayan da aka saki Gomes, ya yi gudun hijira zuwa kasar Portugal. Haka kuma, yanzu sojojin da suka yi juyin mulki sun amince da shawarar da kungiyar ECOWAS ta bayar, ta maido da tsarin dimokuradiyya, amma sun ki amincewa da Raimundo Pereira ya sake zama shugaban wucin gadi na kasar.(Bako)