in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ba za ta tusa keyar Edward Snowden zuwa kasar Amurka ba, in ji Vladimir Putin
2013-06-26 09:51:36 cri

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin wanda yake ziyartar kasar Finland ya nuna a ran 25 ga wata cewa, Rasha ba za ta mika wa Amurka Edward Snowden ba wanda shi ne tsohon ma'aikacin leken asirin kasar Amurka da ya fallasa bayanan asirin kasar ta Amurka.

Bayan ganawar da ya yi tare da shugaban kasar Finland Sauli Väinämö Niinistö, Putin ya bayyana a gun wani taron manema labaru cewa, yanzu Edward Snowden yana yankin matafiyan da ke kan hanyar su ta wucewa na filin saukar jiragen sama dake birnin Moscow, bai shiga kasar ba. Kuma Rasha ba ta taba kulla wata yarjejeniyar tusa keyar wadanda suka aikata laifi zuwa Amurka ba, hakan ya sa, Rasha ba za ta mayar da Edward Snowden ga kasar Amurka ba. Ya ce, hukumar tsaron kasar kuwa ba ta taba hada kai da Edward Snowden ba ko kadan.

Ban da haka, Putin ya nuna cewa, Edward Snowden ya zo kasar Rasha ne ba zato ba tsamani, mutum ne dake da 'yanci, yana fatan Snowden zai sami iznin shiga wata kasa ba tare da wata matsala ba. Kuma yana mai cewa, yana fatan wannan batu ba zai kawo illa ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China