Amurka dai na tuhumar Snowden mai shekaru 30 da laifin cin amanar kasa da satar bayanan gwamnati, sakamakon fallasa dimbim bayanan shirin Amurka na sa-ido kan bayanan wayoyi da na intanet.
Snowden wanda Amurka ke nema ruwa a jallo, ya bar Hong Kong a ranar Lahadi ne ta jirgin sama inda ya sauka a kasar Rasha, an kuma bayar da rahoton cewa, yana neman mafaka a kasar Equador.
Ko da yake wani jami'in kasar Rasha ya fada a ranar Litinin cewa, Amurka ba ta da iznin ta bukaci Rasha ta kama da kuma mika mata Snowden.
A cewar Vladimir Lukin mai rajin kare hakkin bil-adama a kasar Rasha, Snowden bai aikata wani laifi ba a kasar ta Rasha, sannan hukumomin Rasha ba su samu wata bukata daga kungiyar 'yan sanda ta kasa da kasa da ke kama masu laifi ba na neman a kama shi. (Ibrahim)