in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawar Shugaban Sin da na Amurka ta sake jaddada muhimmancin dangantakar kasashen biyu
2013-06-10 16:44:56 cri

Tsohon mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na Amurka Zbigniew Brzezinski, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a ranar Lahadi cewa, ganawar da aka yi tsakanin shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Amurka Barack Obama, ganawa ce mai nasara da ke jaddada muhimmancin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Bayanin na Brzezinski ya zo a bayan ganawar shugabannin ta kwanaki biyu, wadda ta kasance irin ta farko tsakanin jagororin biyu da aka kammala a wurin shakatawar Sunnylands da ke jihar California a ranar Asabar.

Tsohon mai bayar da shawara kan harkokin tsaron na Amurka, ya shaidawa Xinhua cewa, ya gamsu kan yadda dangantakar shugabannin ta kasance mai muhimmanci ga duniya baki daya ganin yadda suka tattauna batutuwa masu fa'ida cikin raha da annashuwa.

Yayin ganawar, shugaba Xi ya bayyana sabon tsarin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta fuskoki guda 3, wato babu fada da kuma takalar juna, mutunta juna da yin hadin gwiwa da za ta kai ga moriyar juna, matakan da tsohon jami'in na Amurka ya ce suna da fa'ida ga kasashen biyu da kuma zaman lafiyar duniya.

Ya ce duk da bambance-bambancen da ke tsakanin kasashen biyu, yana da imanin cewa, kasashen biyu za su yi kokarin daidaitawa a tsakaninsu, bisa la'akari da muhimmancin dangantakar da ke tsakaninsu a bangaren muradunsu na dogon lokaci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China