Kakakin ya bayyana cewa, manyan jami'an kasar Koriya ta Arewa da na Amurka za su tattauna batutuwan sassauta matsanancin halin aikin soja, canja tsarin dakatar da yin yaki a zirin Koriya zuwa tsarin samun zaman lafiya a zirin, da kafa yanayin duniyar maras makaman nukiliya da kasar Amurka ta gabatar da dai sauransu. Ana sa ran kasar Amurka za ta tsara lokaci da wurin da za a gudanar da shawarwarin.
Ban da wannan kuma, kakakin ya ce, idan kasar Amurka tana son kafa duniyar maras makaman nukiliya, kuma sassauta matsanancin halin soja a yanzu, kamata ya yi Amurkan ta yi amfani da wannan dama, ta kuma amsa kiran kasar Koriya ta Arewan. (Zainab)