Bisa umurnin shugaban kasar da Obama ya rattaba hannu a kai, an ce, Amurka za ta saka takunkumi game da hukumomin hada-hadar kudi na kasashen waje wadanda ke yin ciniki da kudin Rial ko kuma account da suka bude a kasashen dake waje da Iran ta hanyar yin amfani da kudin Rial. Wannan shi ne karo na farko da Amurka ta saka takunkumi ga kudaden kasar Iran. Bisa labarin da aka bayar, an ce, tun daga shekarar 2012, takunkumin da Amurka ta sakawa Iran sun haddasa darajar Rial ta ragu da kimanin rabi.
Ban da wannan kuma, Obama ya ba da iznin saka takunkumi ga sana'ar motoci ta Iran, inda ya hana sayar da na'urar motoci da kayayyakin kera motoci ga kasar Iran.
Game da wannan, kakakin fadar White House ta Amurka Jay Carney ya ba da sanarwa cewa, wannan matakin da aka dauka ya kasance kokarin da gwamnatin Obama ta yi don hana Iran ta samu makaman nukiliya, da kara jawo mata wahala wajen takara da kasashen duniya.(Bako)