A cikin sanarwar, majalisar gudanarwar Amurka ta kira Snowden a matsayin mai laifin da ya gudu, ta kuma cewa, an soke fasfonsa ne kafin ya tashi daga HongKong zuwa Moscow. Bayan haka kuma, ta bayyana cewa, bai kamata a amince Snowden shiga ko wace kasa ba, saboda mummun laifin da gwamnatin kasar Amurka ke tuhumarsa da aikata wa a Jumma'a da ta gabata.
Da safiyar ranar Lahadin da ta wuce ne, jami'ai da 'yan majalisar dokokin kasar suka nuna mamaki da fushi game da batun Snowden yayin da suke ganawa da kafofin watsa labaru.
Wasu daga cikinsu sun yi tsamanin rahotannin da Snowden ya bayar sun kawo illa sosai ga kasar Amurka da aminanta, suna fatan gwamnatin Obama za ta cafke Snowden bisa dokokin da suka dace. (Bilkisu)