A ranar 27 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov sun yi shawarwari cikin siri game da shirya taron kasa da kasa kan batun kasar Siriya a birnin Paris da ke kasar Faransa.
Lavrov ya ce, Rasha tana fatan bangaren 'yan adawa na kasar za su dauki hakikanin matakai wajen shirya taron kasa da kasa game da batun Siriya, sabo da Rasha da Amurka suna ganin cewa, bai kamata a gindaya sharadi ba kan shirya taron.
A nasa bangare kuma, Kerry ya ce, abun da suka tattauna a yayin shawarwari na Paris, shi ne tartibin lokacin shirya taron kasa da kasa da tabbatar da wakilan bangaren gwamnatin Siriya da na 'yan adawa na kasar da za su halarci taron. Haka kuma, nan ba da dadewa ba, jami'an ma'aikatar kula da harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha za su shirya wani taron don tattauna hakikanan abubuwan da suka shafi taron.(Bako)