Bisa labarin da aka bayar a shafin internet na shugaban kasar Rasha an ce, bayan shawarwarin, shugaba Putin ya bayar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, shi da Cameron sun tattauna shirin sassauta halin da ake ciki a kasar Syria da kuma yadda za a warware batun Syria. Dukkansu suna fatan za a kawo karshen rikicin kasar Syria cikin hanzari.
Mr Cameron ya bayyana cewa, ko da yake Ingila da Rasha suna da bambancin ra'ayi kan batun Syria, amma burinsu ya yi daidai, wato dakatar da tada rikice-rikice da kuma sa jama'ar kasar Syria da su zabi gwamnatin kasarsa da kansu. Kasar Ingila ta amince da ra'ayin ministan harkokin waje na kasar Rasha Sergei Lavrov da sakataren harkokin waje na kasar Amurka John Kerry game da warware batun Syria ta hanyar siyasa, kana ta nuna goyon baya da a gudanar da taron kasa da kasa kan batun Syria. (Zainab)