in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da babban magatakardan M.D.D. Ban ki-moon da shugaban karba-karba na taron M.D.D Vuk Jeremic
2012-09-25 16:24:12 cri

A ranar 24 ga wata da yamma, a birnin New York hedkwatar M.D.D., ministan harkokin wajen kasar Sin Mr. Yang Jiechi ya gana da babban magatakardan M.D.D Ban ki-moon da shugaban karba-karba na taron M.D.D karo na 67 Vuk Jeremic.

 

A jawabinsa, Yang Jiechi ya ce, a karkashin yanayin da ake ciki yanzu, kasashen duniya sun dora muhimmanci sosai game da M.D.D., don haka kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga majalisar don ta kara taka rawar a zo a gani wajen samun zaman lafiya da sa kaimi ga samun bunkasuwa, da cimma burin samun ci gaba cikin dogon lokaci, da kuma cimma burin raya kasa da aka tsara a shekara ta 2000.

 

A nasu bangare, daya bayan daya, Ban ki-moon da Vuk Jeremic sun nuna godiya ga kasar Sin don nuna goyon baya ga aikin M.D.D, kuma suna fatan kasar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa a wannan fanni, kana M.D.D. tana fatan inganta hadin gwiwa da kasar Sin, don sa kaimi ga kasashen duniya da su cimma burin raya kasa da aka tsara a shekara ta 2000, da kokarin warware batutuwan duniya da na shiyya-shiyya, don sa kaimi ga samar da zaman lafiya da bunkasuwa a kasashen duniya.(Bako)

 

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China