in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi Allah wadai da satar masu kiyaye zaman lafiya a kasar Sudan
2012-02-21 17:23:30 cri
Game da lamarin da ya abku a yankin Darfur na kasar Sudan kwanakin baya inda aka saci wasu masu kula da aikin wanzar da zaman lafiya na MDD, Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin, ya furta a ranar 21 ga wata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, cewa Sin ta yi Allah wadai da aikace-aikacen nuna karfin tuwo da aka yi wa sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD.

A wajen wani taron manema labaru da aka kira a wannan rana, Mista Hong Lei ya ce, kasar Sin, kamar yadda ta saba yi, za ta ci gaba da nuna goyon baya ga sojojin wanzar da zaman lafiya na hadin kan MDD da tarayyar kasashen Afirka don su gudanar da aikinsu a yankin Darfur bisa ikon da wani kuduri mai lamba 2003 da kwamitin sulhun MDD ya zartas ya ba su. Kana kasar Sin za ta tsaya kan wata manufa ta mai da hankali kan girke sojojin kiyaye zaman lafiya tare da kokarin aiwatar da matakan siyasa don neman tabbatar da zaman lumana, kwanciyar hankali da ci gaba a yankin Darfur tun da wuri.

Labarin da aka bayar ya bayyana cewa, a kwanakin baya, dakaru masu adawa da gwamnati na kungiyar JEM sun sace masu kiyaye zaman lafiya 52 da MDD da kungiyar AU suka girke a yankin Darfur, daga bisani an saki 49 daga cikin mutanen da aka sata. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China