Mr. Xie wanda ya fadi haka a gun taron manema labaru na Sin da kasashen waje da ma'aikatar harkokin waje ta kasar ta shirya ,ya bayyana fatansa cewa, taron zai bi tunani da ka'idar Rio, musamman ma tsarin daukar nauyi daya amma da bambanci, a kokarin sa kaimi ga ra'ayoyin kasa da kasa na kara karfin siyasa, da tabbatar da yarjeniyoyin da aka kulla daga shekarar 1992 zuwa ta 2002 a dukkan fannoni, da tsara hakikanin shirin gudanarwa a bayyane, da kuma tabbatar da cika alkawarin wasu kasashen sukuni na ba da kudin agaji, da yin musayar fasahohi, da kara kwarewa da dai sauransu.
Ban da haka, Mr. Xie ya ce Sin na fatan babban taron zai zartas da wani bayanin sakamako mai inganci, a kokarin bayyana ra'ayoyin bangarori daban daban a fannin siyasa, da daidaita batutuwan da kasashe masu tasowa suke mai da hankali a kansu, a kokarin ba da jagoranci ga hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a nan gaba.
An ce, firaministan kasar Sin Wen Jiabao zai jagoranci kungiyar wakilan kasar don halartar taron, kuma zai yi muhimmin jawabi a gun taron. (Fatima)