Mr. Li ya bayyana haka ne lokacin ya ke jawabi a taron muhawara na kwamitin sulhu na MDD kan inganta tsaron iyakoki. Yana mai cewa, " a baya-bayan nan yaduwar makamai a yammacin Afirka da yankin Sahel da kuma juyin mulki a kasar Mali ya jawo hankalin duniya matuka."
Li ya ce kamata ya yi hadin gwiwar kasa da kasa ya mayar da hankali kan taimakawa kasashen da ke bukatar kara karfinsu. Ya kuma lura da cewa, batun kula da kan iyaka batu ne na kasashen da abin ya shafa, kuma hakkin gwamnatocin kasashen ne su inganta tsaron iyakoki da dokokinsu na kwastan, tare da yaki da dukkan wasu nau'o'in safara da zirga-zirgar a kan iyaka da suka sabawa doka.
A wani labarin kuma, a ranar Laraba ne babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya jaddada bukatar samar da matakan da suka dace don taimakawa kasashe su sa-ido,kare tare da kiyaye kan iyakokinsu daga shigowar kayayyaki da jama'a ba bisa ka'ida ba, yana mai bayyana yadda MDD ta ke taka muhimmiyar rawa ta wannan fanni.
A ranar Laraba ne majalisar mai mambobin kasashe 15 ta gana inda ta yi muhawara kan yadda wannan batu ke kawo barazana ga zaman lafiya da tsaro, al'amarin da ke sanya MDD ta kara karfinta na taimakawa kasashe su magance wannan matsala.(Ibrahim)