A lokacin da ya gabatar da wani jawabi a yayin bikin murnar cika shekaru 66 da kafuwar majalisar dinkin duniya da aka shirya yau, Mr. Wu ya ce, a halin da ake ciki yanzu a duniya, batutuwan tsaron kai irin na gargajiya da wanda ba irin na gargajiya ba suna bullowa tare, ba ma kawai M.D.D. take da nauyin tabbatar da zaman lafiya a duniya ba, har ma tana da nauyin neman ci gaba da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa.
Sannan Wu Hailong ya nuna cewa, kasar Sin tana bukatar goyon baya daga wajen M.D.D. domin neman ci gaba, haka kuma, M.D.D. tana bukatar kasar Sin da ta kasance kan harkokin kasa da kasa, wannan zabi ne da aka yi bisa hanyar neman ci gaba da kasar Sin take bi. Kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan hanyoyin bude kofarta da yin hadin gwiwa da kuma neman ci gaba tare da sauran kasashen duniya ba. Kasar Sin ta zabi hanyar neman ci gaba cikin lumana ba zabi ne da ta yi a wani lokaci domin wani al'amari ba, wannan zabi ne da ta yi domin dacewa da zamani, da kuma kokarin bayar da karin gudummawarta wajen ci gaban wayin kai na kasa da kasa. (Sanusi Chen)