Li Baodong, wanda shi ne wakilin din-din-din na kasar Sin a MDD ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a wajen wani taron kwamitin sulhun kan yaki da ta'addanci.
Li ya ci gaba da cewa kasar Sin na mai nuna kin amincewarta ga ta'addanci ta kowace fuska, bayan da shugabannin kananan kwamitocin kwamitin tsaron na MDD suka gabatar da jawabi kan batun.
Ya kara da cewa suna fata wadannan kwamitoci za su ci gaba da tattaunawa da kasashe mambobi, su kara inganta hadin gwiwa da sauran cibiyoyin MDD, kana a taimakawa kasashe mambobi musamman ma kasashe masu tasowa, domin a samu inganta aikin yaki da ta'addanci.
Jakadan na kasar Sin ya kuma jadadda cewa ko kadan kasar Sin bata amince da yin baki biyu ba kan yaki da ta'addanci. (Bilkisu)