in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta karfafa hadin kai tare da MDD
2010-10-31 17:17:47 cri
A ranar 30 ga wata a birnin Shanghai, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya yi shawarwari tare da babban sakataren MDD, Ban Ki-Moon, inda ya bayyana cewa, kasar Sin za ta karfafa hadin kai tare da MDD.

A cikin shawarwarin, Yang Jiechi ya nuna yabo ga muhimmiyar rawar da MDD ke takawa a cikin harkokin duniya, kuma ya bayyana cewa, ko da yaushe kasar Sin na nuna goyon baya da sa himma wajen shiga ayyukan MDD, kana tana son karfafa yin cudanya da hadin gwiwa tare da MDD, da kuma goyawa babban sakataren MDD baya wajen gudanar da ayyukansa.

A nasa bangaren kuma, Ban Ki-Moon ya yi godiya ga goyon bayan da kasar Sin ke nunawa MDD da kuma shi da kansa, ya kara bayyana cewa, MDD tana fatan karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin. Bayan haka kuma, Ban Ki-Moon ya taya kasar Sin murnar nasarar shirya bikin baje koli na duniya, ya bayyana cewa, bikin baje kolin ya burge shi sosai.

Dadin dadawa, bangarorin biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan batutuwan muradun karni na MDD, sauyin yanayi, da kuma matsalolin duniya da na shiyya-shiyya. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China