in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasar Somaliya da ta samun sulhuntawa a tsakanin kabilu
2012-05-16 10:55:59 cri
A ranar 15 ga wannan wata a cibiyar MDD dake birnin New York, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min ya jaddada cewa, samun sulhuntawa a tsakanin kabilu ita ce hanya daya kawai ta maida zaman lafiya a kasar Somaliya.

A wannan rana, kwamitin sulhu ya gudanar da wani taro a bainar jama'a kan batun kasar Somaliya. Inda Wang Min ya ce yana fatan bangarori daban daban na kasar Somaliya za su dora muhimmanci kan moriyar kasar da ta jama'a, da warware rikici ta hanyar yin shawarwari cikin hanzari, ta haka za a magance kawo cikas ga shimfida zaman lafiya a kasar. Ya kara bayyana cewa, kasar Sin ta nuna goyon baya ga gwamnatin wucin gadin kasar Somaliya da ta kara inganta karfinta da sarrafa harkokin kasar ba tare da bata lokaci ba. Kana tana fatan kungiyoyi daban daban na kasar Somaliya da su yi watsi da tada rikici tare da shiga aikin shimfida zaman lafiya ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Hakazalika kuma Wang Min ya yi kira ga kasa da kasa da su ci gaba da nuna goyon baya ga MDD da kungiyar AU da kuma hukumar raya kasashen gabashin Afirka wato IGAD a kokarin da suke yi na aikin shiga-tsakani don taimakawa hukumar wucin gadi ta kasar Somaliya ta inganta karfinta da sa kaimi ga bangarori daban daban na kasar da su aiwatar da taswirar shimfida zaman lafiya a kasar da aka cimma.

A ranar 15 ga wannan wata, kwamitin sulhu na MDD ya bayar da wata sanarwa, inda ya kalubalanci bangarori daban daban na kasar Somaliya da su yi namijin kokari wajen kawo karshen wa'adin hukumar wucin gadi cikin lokaci, da kuma bukace su da cimma daidaito kan yadda za a aiwatar da wasu ayyuka bayan wannan lokaci.

Ban da wannan kuma, hukumar samar da abinci ta duniya ta sanar a birnin Geneva a ranar 15 ga wata da cewa, hukumar za ta yi amfani da shirin raba tikitin abinci wajen bada gudummawar abinci ga wasu yankunan kasar Somaliya a madadin bada abinci kai tsaye da aka aiwatar a dogon lokaci.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China