in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministocin harkokin wajen kasashen Sin da Amurka sun yi hira ta wayar tarho
2013-03-21 17:21:25 cri

Ministan harkokin wajen kasar Sin mista Wang Yi da takwaransa na kasar Amurka mista John Forbes Kerry sun yi hira ta wayar tarho a ranar 20 ga wata da dare.

A cikin wannan hira, Wang Yi ya nuna cewa, a cikin shekaru 34 da suka gabata tun bayan kulla dangantakar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka, kasashen biyu sun samu ci gaba sosai wajen raya dangantakar dake tsakaninsu. Ya zuwa yanzu, ana fuskantar sabon zarafi wajen raya dangantakar dake tsakaninsu, ya kamata mu kara samu ci gaba bisa harsashin da aka aza a baya. Ko da yake, kasashen biyu na fuskantar wani muhimman batu wanda ya shafi yadda shugabannin kasashen biyu za su tabbatar da raya dangantakar hadin kai tsakanin kasashensu cikin sahihanci da kuma kafa sabuwar dangantakar tsakanin manyan kasashe ta yadda za su amsa bukatun duniya, ya ce, ya kamata a fara wannan aiki daga yankin Asiya-Pacific.

A nasa bangare kuwa, John Forbes Kerry ya ce, kasashen biyu na samun dama mai kyau wajen raya dangantakar dake tsakaninsu, duk da cewa akwai bambancin ra'ayi, amma yawan fannonin hadin gwiwa ya fi na bambanci nisa ba kusa ba. Amurka na fatan kara yin mu'amala da kasar Sin ta yadda za su kara raya dangantakar dake tsakaninsu ta yadda za su ba da misali mai kyau na musayar ra'ayi a matsayinsu na manyan kasashe.

Haka kuma, jami'an biyu sun tattauna kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda halin da ake ciki a zirin Korea, sauyin yanayi, tsaron Intarnet da sauransu. Kuma Wang Yi ya bayyana matsayin da Sin take dauka kan wadannan batutuwa. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China