Za a daidaita saurin karuwar GDP ta yadda zai yi daidai da saurin karuwar yawan cinikin waje na Sin a shekarar 2013
A ranar 16 ga wata, a gun taron manema labaru da aka saba yi a nan birnin Beijing, kakakin ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci Shen Danyang ya bayyana cewa, a shekarar 2012, yawan bukatun sayayya daga kasashen waje bai yi yawa kamar yadda aka zato ba, a shekarar 2013, za a ci gaba da fuskantar yanayi mai tsanani wajen raya cinikin waje, kuma babban burin da aka saka a gaba shi ne, tabbatar da saurin karuwar cinikin waje ta yadda zai yi daidai da saurin karuwar GDP, da kasar Sin za ta samu a harkokin cinikin kasa da kasa.
Bisa sabuwar kididdigar da hukumar kwastam ta yi, an ce, a shekarar 2012, jimillar kudin da Sin ta samu wajen shige da ficen kayayyaki ta kai dalar Amurka biliyan 3866.76, abin da ya karu da kashi 6.2 cikin 100.
Game da rashin cimma burin da aka yi na samun saurin karuwar cinikin kasashen waje da yawansa ya kai kashi 10 cikin 100, Shen Danyang ya bayyana cewa, a karkashin yanayi na saurin karuwar cinikin duniya da ya kai kashi 2.5 cikin 100, saurin karuwar cinikin waje da Sin ta samu ya kai kashi 6.2 cikin 100 wanda yake a sahun gaba a duniya.(Bako)