in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta samu cigaba ta fuskar hada-hadar shige da fice a watan Satumba
2012-10-15 11:18:01 cri
Hukumar kwastan ta kasar Sin ta bayar da kididdiga a kwanan baya cewa, halin da Sin ke ciki a fannin cinikayyar shige da fice a watan Satumban bana ta sami habaka. Yawan kudin da ta samu ta fuskar fitar da kayayyaki cikin wata daya ya kai sabon matsayi wanda saurin karuwarsa ya dan dara idan an kwatanta shi bisa na bara war haka. Ban da wannan kuma, saurin karuwar cinikin shigo da kayayyaki ya samu ci gaba inda an kwatanta shi bisa na bara war haka.

Bisa kididdigar da jami'in ya bayar, an ce, a cikin watanni 9 da suka gabata na bana cinikayyar shige da fice ta kasar Sin ta fuskanci sauye-sauye iri gudu uku, da farko, saurin karuwar cinikayyar shige da fice a fannin kayayyaki da aka harhada, ya fi samun saurin habaka. Na biyu, Sin ta samu ci gaba sosai wajen yin ciniki da muhimman abokanta, kuma kasuwanni masu tasowa sun samu ci gaba sosai. Na uku, yankin tsakiya da na yamma sun sami ci gaba cikin sauri, musamman ma wajen fitar da kayayyaki, yayin da yankin gabas ya samu matsakaicin ci gaba.

Wani manazarci ya nuna cewa, a tsakiyar watan Satumba, majalisar gudanarwa ta kasar ta zartas da sabbin manufofi guda 8 game da tabbatar da ci gaban hada-hadar shige da fice, wadanda za su yi amfani wajen kyautata halin da Sin take ciki a wannan fanni. Bugu da kari, bukukuwan ranar kirsimeti da na sabuwar shekara na karatowa, hakan ya sa, watan Satumba ya zama wata mai amfani ga kamfanonin fitar da kayayyaki na kasar. Wannan ya nuna cewa, ci gaban da ake samu na da alaka da yanayi ko halin da ake ciki.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China