A kuma watan Janairu na shekarar ta bana, adadin cinikayyar ketare da ke tsakanin Sin da manyan abokan cinikayyarta da suka hada da kungiyar tarayyar kasashen Turai, kasar Amurka, kungiyar tarayyar kasashen Asiya ta kudu maso gabas da kuma kasar Japan ya karu, musamman ma tsakanin Sin da kungiyar tarayyar kasashen Asiya ta kudu maso gabas, inda adadin ya karu da kashi 40 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
A watan Janairu, adadin hajojin injuna masu amfani da lantarki da Sin ta fitar zuwa kasashen ketare ya kai darajar daruruwa biliyan na dallar Amurka, yayin da hajojin kananan masana'antu na manyan abubuwa iri bakwai, kamar su kayayyakin saka, tufafi, takalma, kayayyakin daki, da dai sauransu ya kai wajen dallar Amurka biliyan 42.
Bugu da kari, yawan rairayi na bakin karfe, kwal da kuma kayayyakin bakin karfe da Sin ta shigo ya karu, amma yawan jan karfe da motoci da Sin ta shigo da su ya ragu. (Maryam)