in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan kudin da kasar Sin ta samu wajen cinikin shigi da fici ya karu da kashi 6.2 bisa dari a shekarar 2012
2013-01-10 15:59:14 cri
Bisa kididdigar da babbar hukumar kwastan ta Sin ta bayar ran 10 ga wata, an ce, gaba daya yawan darajar hajjojin da Sin ta fitar zuwa kasashen ketare da kuma wanda aka shigo da su daga kasashen waje cikin shekarar 2012 ya kai dallar Amurka biliyan 3866.76.

Adadin ya karu da kashi 6.2 bisa dari idan aka kwatanta da na bara waccan. Adadin hajjojin da Sin ta fitar zuwa kasashen ketare ya karu da kashi 7.9 bisa dari, yayin da yawan hajojin da Sin ta shigo da su ya karu da kashi 4.3 bisa dari. Bugu da kari, yawan rarar kudin da kasar Sin ta samu wajen cinikayya tsakaninta da kasashen ketare ya kai dallar Amurka biliyan 231.1. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China