in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na kokarinta wajen nuna goyon baya kan masana'antun cinikin waje
2012-09-12 16:22:47 cri
Mai ba da taimako ga ministan cinikayya na kasar Sin, Yu Jianhua ya bayyana a jiya Talata a nan birnin Beijing cewa, kasar Sin a yanzu haka na fuskantar yanayi mai tsanani a fannin cinikin waje, yanzu kuma gwamnatin kasar na kokarin kyautata muhallin ciniki, da nuna goyon baya ga masana'antun cinikin waje.

Yu ya kara da cewa, sakamakon tasirin da rashin farfadowar tattalin arzikin duniya, da matsalar basussuka ta Turai ke kawowa, kasar Sin na cikin wani yanayi mai tsanani ta fuskar cinikayya a bana. Tun bayan da aka shiga watan Yuli, kasar Sin ta samu tabarbarewar cinikin waje, a watan Agusta kuma jimillar kudin da kasar ta samu wajen cinikin waje ta kai dalar Amurka biliyan 329.29, wato ta karu da kashi 0.2 cikin kashi 100 kawai. Masana'antun cinikin waje na wasu yankunan dake bakin teku na kasar Sin, ciki har da birnin Shanghai, lardin Fujan, birnin Shenzhen da sauransu suna fuskantar matsalolin raguwar bukatun kayayyaki, da karuwar yawan kudaden da ake kashewa wajen samar da kayayyaki.

Game da batun, Yu ya bayyana cewa, yanzu lokaci mai kyau ya yi da gwamnatin kasar Sin za ta dauki matakan da suka dace don nuna goyon baya ga masana'antun cinikin waje. Yanzu hukumomin dake da nasaba da cinikayya suna kokarin nazarin manufofi da matakai a jere da nufin nuna goyon baya ga bunkasuwar cinikin waje yadda ya kamata, da kuma kyautata yanayin cinikayya, da taimakawa masana'antun cinikin waje wajen kawar da matsaloli. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China