Ma'aikatar kasuwancin kasar Sin ta sanar a ranar 26 ga watan nan cewa, matakan da kasar Sin ta fara dauka na canza tsarin cinikayya da kasashen waje sun yi amfani. Inda a farkon watanni 9 na shekarar 2012, saurin karuwar yawan fitar da kayayyakin kasar Sin ya wuce na sauran kasashe masu karfin tattalin arziki, wanda hakan ya sanya kason kasar a duniya ta fuskar cinikayya ya karu zuwa kashi 11.1%, idan an kwatanta da na shekarar 2011.
Idan an yi nazarin sauyawar yanayi da ake samu a nan kasar Sin a fannin ciniki, za a ga cewa, kasar na kokarin fitar da nagartattun kayayyaki, bisa hanyoyi masu sauki da dacewa, kana tana kokari wajen samar da wasu fitattun alamomi na kamfanoni masu samar da kaya. (Bello Wang)