Kasar Amurka ta kasance ta farko a rukunin kasashe 60 masu karfin tattalin arziki na duniya na shekara ta 2013, kasar Switzerland na biye da ita, yayin da yankin Hong Kong na kasar Sin mai tsarin mulki na musamman ya zo na uku, kamar yadda makarantar nazarin harkokin kasuwanci ta kasar Switzerland IMD ta bayyana cikin rahotonta.
Rahoton shekara-shekara na makarantar ta IMD da aka fitar a ranar Alhamis, ya nuna cewa, kasar ta Amurka ta samu wannan matsayi a wannan shekara ne bayan ta zo ta biyu a shekara ta 2012, sakamakon farfadowar harkokinta na kudi, karuwar fasahar kirkire-kirkire, da kuma ci gaban kamfanoni da aka samu a kasar
Bugu da kari a yankin Asiya, shi ma babban yankin kasar Sin da kuma kasar Japan, sun samu ci gaban maki 2 da kuma 3, inda suka kasance a mataki na 21 da kuma 24 bi da bi.
A halin da ke ciki, tattalin arzikin kasashen da ke kungiyar BRICS ya samu ci gaba, inda rahoton ya nuna cewa, tattalin arzikin kasashe masu tasowa, ya dogara kwacakwam kan yadda tattalin arzikin kasashe masu ci gaba zai farfado, amma a cewar darektan IMD Stephane Garelli, kasashen na BRICS sun kasance wuraren da ke da makoma mai haske.(Ibrahim)