in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wadanda ake zargi da ta da bom a Boston sun so su kai hari a New York
2013-04-26 10:22:18 cri

Mutane biyu da ake zargi da ta da bom a Boston sun so su je birnin New York na kasar Amurka ne don su dasa bom a filin Time Square, in ji magajin garin New York Michael Bloomberg yayin wata ganawa da ya yi da 'yan jarida ranar Alhamis.

Yayin ganawa da 'yan jarida ta hadin gwiwa da kwamishinan 'yan sanda a New York Raymond Kelly, magajin garin na New York ya ce, birnin ne inda suka nufa da harin.

Ya kara da cewa, har yanzu birnin New York ne inda masu kin jinin Amurka ke son su kawo hari.

Kelly ya bayyana cewa, bisa abin da aka gano bayan bincike, wadanda ake zargin su biyu sun shirya tuka mota zuwa birnin New York bayan da suka kwace wata mota a Boston da kuma sauran ababan fashewan za su je filin Time Square da su ne.

A fadar Kelly, wanda ake zargin 'dan shekaru 19 Dzhokhar Tsarnaev ya bayyana wa masu masa tambayoyi a asibiti da ake jinyarsa a Boston cewa, shi da yayansa Tamerlan Tsarnaev sun shirya a daren ranar 18 ga wata su tafi birnin New York su ta da ababan fashewa, da bom din tukunyar girki da na bututu a filin Time Square.

To amma, wannan shiri nasu bai cimma buri ba domin mota da suka kwace ba ta da isashen mai.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China