A yunkurinsa na yiwa manufofin yakin da ta'addanci kwaskwarima, shugaba Obama na Amurka ya gabatar da sabbin manofofin game da amfani da jiragen yakin kasar, tare da sake alkawarta rufe gidan yarin nan na Guantanamo. Shugaba Obama ya bayyana wadannan manufofi ne ranar Alhamis 23 ga wata, yayin wani taron bayyana manufofi da ya gabata a ma'aikatar tsaron kasar.
A cewarsa, sabbin manufofin na da burin rage hare-haren da kan jawo cece-kuce. Yana mai cewa, ya zuwa shekarar 2014, Amurka za ta janye dukkanin sojojinta daga Afghanistan, ganin yadda aka ci karfin kungiyar Al-Qaeda a sassan kasar. Shugaba Obama ya ce, baya ga kasar ta Afghanaistan, Amurka ta kuduri aniyar daukar matakan tsare, tare da bincikar 'yan ta'adda, da ma kai hari a wuraren da babu wata gwamnati da ke da karfin dakile ayyukan ta'addanci, ko barazanar 'yan ta'adda.
Cikin jawabin nasa, Obama ya gabatar da wata bukata ga majalissar dokokin kasar, ta janye takunkumin sauyawa firsinoni wuraren tsaro, musamman daga gidan yarin Guantanamo zuwa wasu gidajen yarin, a hannu guda kuma ya bukaci ma'aikatar tsaron kasar, da ta fidda wani wuri a cikin kasar da za a kebe, domin ya zamo sashen lura da harkokin soji, yana mai alkawarin tura wakili da zai sanya ido kan aikawa da firsinoni zuwa kasahensu, a lokacin da ake burin dage dokar da ta hana mika firsinoni zuwa kasar Yemen.(Saminu)