Wakilai fiye da 860 na gwamnatoci, da sassan masana'antu da na masana da suka fito daga kasashe fiye da 70 ne suka halarci wannan taron tsawon kwanaki 3, ciki had da shugabanni 12 na kasashen Afirka. Babban taken taron shi ne cika alkawarin da kasashen Afirka suka yi. Kuma nufin gudanar da taron shi ne kara azama kan bunkasuwar tattalin arzikin Afirka, gaggauta gudanar da ayyukan more rayuwar al'umma a Afirka bisa manyan tsare-tsare, da kara karfin horas da kwararru a Afirka.
A cikin jawabansu a yayin taron, wakilai da dama sun nuna cewa, a cikin shekaru 10 da suka wuce, Afirka ta samu ci gaban tattalin arziki sosai, amma ya zuwa yanzu nahiyar tana fuskantar kalubaloli da dama wajen raya tattalin arziki.
Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya ce, bai kamata ba kasashen Afirka su dinga dogaro da kasashen waje domin samun isasshen kudi. Hanya mai kyau ita ce gaggauta raya tattalin arzikin yankin Afirka baki daya. (Tasallah)