in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Masar da ministan tsaron Amurka sun gana dangane da hadin gwiwa a fuskar soji da batun Syria
2013-04-25 15:30:40 cri

A ranar Laraba ne shugaban kasar Masar Mohammed Morsi ya gana da ministan harkokin tsaron kasar Amurka Chuck Hagel, wanda ke ziyara a Masar, inda suka tattauna kan hadin gwiwa a fuskar soji da kuma yadda abubuwa suke a kasar Syria.

Kamfanin dillancin labaran kasar Masar, MENA, ya ba da rahoto bisa wata sanarwar da ta fito daga fadar shugaban kasar cewa, shugaba Morsi da Hagel sun tattauna kan bunkasa hadin gwiwa a fannin soji tsakanin kasashen biyu don moriyar juna.

A halin da ake ciki kuma, shugaban kasar Masar ya yi gargadi dangane da barazanar ci gaban rikici a kasar Syria, wanda zuwa yanzu ya yi sanadin salwantar rayukan dubban fararen hula.

Tun da farko a ranar Laraban, ministan harkokin tsaron kasar Masar Abdel-Fattah Al-Sisi ya gana da Hagel dangane da bunkasa hadin gwiwar soji tsakanin kasashen biyu.

Hagel ya iso birnin Alkahira ranar Laraba daga babban birnin kasar Saudiya, Riyadh a matsayin wani bangaren ziyara da yake a gabas ta tsakiya.

Manufar wannan ziyara da Hagel yake yi shi ne kara bunkasa hadin gwiwar soji da kawayen Amurka a yankin, ciki har da kasashen Isra'ila, Saudi Arabia, Jordan da kuma Masar, don nuna musu goyon baya, dangane da abin da rikicin Syria ke iya haifarwa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China