in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin Zimbabwe na raguwa, a cewar ministan kudin kasar
2013-05-29 10:38:54 cri

Ministan tattalin arzikin kasar Zimbabwe, Tendai Biti, ya fada a ranar Talata cewa, tattalin arzikin kasar yana raguwa, don haka akwai bukatar gwamnati ta yi karin haske game da ranar da za a gudanar da zaben kasar, ta yadda za a baiwa 'yan kasar tabbaci.

Bugu da kari, Biti ya ce, kamfanonin da ke hakar zinari a gabashin kasar ba su biya kudin haraji ba a cikin watanni hudu na farkon shekara, matakin da ya ce ba za a amince da shi ba.

Shi dai Biti wani jigo ne a jam'iyyar MDC-T ta firaminista Morgan Tsvangirai da zai fafata da shugaba Robert Mugabe a zaben shugaban kasar da za a yi.

Ko da ya ke duk da rashin biyan harajin daga bangaren kamfanonin da ke hakar ma'adinai a kasar, Biti ya ce, yana da tabbacin cewa, za a samu dala miliyan 113 da ake bukata wajen gudanar da zabukan kasar.

Ya ce, kasar ta Zimbabwe tana sa ran samun taimako daga MDD, kana sun rubuta wa SADC da daidaikun kasashe kamar Afirka ta Kudu da Angola takardar neman taimakon kudi. Ya kuma ce, jama'a na son taimakawa kasar Zimbabwe, kamar yadda suka nuna irin abubuwan da za su yi a lokacin shirin kuri'ar jin ra'ayin jama'a da kuma rijistan kundin masu zabe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China