in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Amurka na duba yiwuwar baiwa 'yan adawar Syria taimakon makamai
2013-05-02 14:26:45 cri

Jaridar 'Washington Post' ta kasar Amurka ta ba da rahoto a ranar Laraba cewa, gwamnatin Obama na duba yiwuwar baiwa dakarun 'yan adawar Syria tallafin makamai, kuma ana sa ran a yanke wannan shawara cikin makonni.

Jami'ai sun bayyana cewa, suna kokarin ganin an yi jigilar makaman, amma sun jaddada cewa, har yanzu suna kokarin ganin an sasanta a siyasance.

Bayanan da aka samu game da canjin manufa a fadar ta 'White House', ta zo ne bayan da kasar ta Amurka ta bi sahun kasashen Faransa, Burtaniya, da Isra'ila a makon da ya gabata, wajen tabbatar da cewa, an yi amfani da makamai masu guba a rikicin na Syria da aka shafe shekaru 3 ana yi, kana sama da mutane 70,000 suka mutu.

Ko da ya ke kasar ta Amurka ta ce, ba ta san yadda aka yi amfani da makaman, lokacin da aka yi amfani da su da kuma wanda ya yi amfani da su ba.

Shugaba Obama ya kuma yi gargadi a ranar Laraba game da hanzarin yanke hukunci game da batun amfani da makamai masu guba din a Syria, inda ya ce, yana bukatar hujjoji masu gamsarwa kafin daukar wani mataki.

Jaridar ta 'Washington Post' ta ce, gwamnatin Amurka tana kokarin gamsar da shugaba Putin na Rasha cewa, yiyuwar amfani da makamai masu guba da gwamnatin Syria ta yi, da karin shisshigi daga ketare da zai ruru wutar rikici, da har ya kamata ya goyi bayan gwamnatin Assad.

A mako mai zuwa ne aka shirya sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry zai ziyarci kasar Rasha, haka kuma Obama zai gana da shugaba Putin na Rasha da farko a watan Yuni, yayin da shugabannin kungiyar kasashen G8 za su gana a arewacin Ireland, kana za su sake ganawa a watan Satumba a kasar Rasha.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China