in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A kalla mutane 17 ne suka jikkata a bikin ranar mahaifiya da aka yi a Amurka
2013-05-13 10:46:14 cri

Kafofin watsa labaran Amurka sun bayyana cewa, a kalla mutane 17 ne suka ji rauni a ranar Lahadi, lokacin da wasu 'yan bindiga suka bude wuta a wajen wani fareti da aka shirya a ranar tunawa da mahaifiya a jihar New Orleans ta Amurka.

Gidan talabijin na CNN ya ruwaito kakakin 'yan sanda Remi Braden, tana cewa, rayuwar wadanda suka ji bata cikin hadari. Ta kuma ce, wannan abu ne da ba su saba gani ba, ta kuma ba da tabbacin cewa, za su cafke wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Safritandan 'yan sanda Ronal Serpas ya ce, da alamun mutane biyu ko uku ne haka kawai suka fara bude wuta a kan taron jama'a.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China