in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya zata dauki nauyin shirya dandalin tattaunawa kan harkokin tattalin arziki na duniya kan Afirka
2013-05-12 16:41:09 cri

A shekara mai zuwa ne Najeriya zata shirya dandalin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki na kasa da kasa, kan nahiyar Afirka karo na 24 a Abuja, babban birnin tarayyar kasar.

Ministar kula da harkokin tattalin arziki da hada-hadar kudi ta Najeriya, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ce ta fadi hakan, a wajen bikin rufe dandalin tattaunawa kan harkokin tattalin arziki na duniya karo na 23, wanda aka yi a ranar Jumma'ar da ta gabata a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta yi godiya bisa zabar Najeriya da aka yi, domin bata damar shirya wannan gagarumin taro a shekara mai zuwa, inda ta ce, hakan ya dace da yanayin bunkasar tattalin arzikin Najeriya a 'yan shekarun nan.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta kara da cewa, Afirka na fuskantar ci gaba, da kalubale a sa'i daya, ciki har da rashin ingantattun ababen more rayuwar jama'a, rauni na fannin tafiyar da mulki, cin hanci da rashawa da sauransu. Sai dai duk da haka kasashen na Afirka na da makoma mai haske, musamman ma a fannin tattalin arziki da cinikayya, saboda irin kwazon da manyan shugabannin kasashen na Afirka suke nunawa a wannan taron dandalin tattaunawa.

Har wa yau kuma a nasa bangaren, babban daraktan dandalin tattauna batutuwan tattalin arzikin Najeriya Mista Frank Nweke Jnr yayi cewa, Najeriya tana farin-ciki sosai da samun damar shirya wannan taro a shekara mai zuwa. Ya kuma bayyana cewa, shugaba Goodluck Jonathan ya riga ya dankawa wani rukuni izini, don shirya taron dandalin tattaunawar cikin nasara a shekarar dake tafe.(Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China