in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An tafi da wanda ake zargi da dasa bom a Boston zuwa asibitin gidan yari
2013-04-27 15:58:30 cri

An dauke wanda ake zargi da dasa bom a Boston wanda ya samu rauni, daga wani asibiti zuwa asibitin gidan yari, in ji jami'an 'yan sandan kasar Amurka ranar Juma'a.

A fadin mai magana da yawun jami'an 'yan sanda Drew Wade, an tafi da Dzhokhar Tsarnaev, 'dan shekaru 19, wanda ake zargi da dasa bom, daga asibitin Beth Israel Deaconnes, zuwa asibitin tarayya na Devens.

Asibitin gidan yarin yana cikin harabar tsohuwar cibiyar soji ta Fort Devens, kuma an tsarata ne domin 'yan fursuna dake bukatar jinya.

Tsarnaev ya samu raunin bindiga a makogwaronsa, kuma ana masa jinya tun lokacin da aka kama shi ranar Juma'a da ta gabata.

Tsarnaev dai, ana zarginsa ne da dasa tagwayen bom ranar 15 ga watan Aprilu a wajen tseren yada-kanen-wani na garin Boston, inda mutane uku suka mutu, kana sama da 200 suka samu rauni. Yayansa, Tamerlan wanda shi ma ana zarginsa ya rasa ransa a yayin musayar wuta da jami'an 'yan sanda a lokacin da ake farautarsu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China