in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya fara ziyara a kasar Pakistan
2013-05-22 16:54:58 cri
Da safiyar yau Laraba 22 ga wata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya isa birnin Islamabad, hedkwatar kasar Pakistan, domin fara ziyarar aiki.

Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari, da firaministan Raja Pervaiz Ashraf sun tarbe shi a filin saukar jiragen saman kasar, inda aka shirya kasaitaccen biki domin maraba da shi.

Bisa labarin da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bayar, an ce, a yayin wannan ziyara, Li Keqiang zai yi shawarwari da Asif Ali Zardari, da Raja Pervaiz Ashraf, tare kuma da ganawa da shugabannin majalisu, da na jam'iyyun siyasa da kuma na sojin kasar, har ila yau zai yi jawabi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Pakistan, sannan zai tuntubi bangarori daban-daban na al'ummar kasar ta Pakistan, ciki hadda mutanen dake sada zumunci da kasar Sin.

Li Keqiang yana wannan ziyara ne a daidai lokacin da Pakistan ta kammala babban zabenta, tare da fara kafa sabuwar gwamnatinta, a ganin mataimakin ministan harkokin waje na kasar Sin Song Tao, wannan ziyara ta shaida amincewa da juna, da kuma dankon zumunci dake tsakanin kasahen biyu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China