Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Indiya wajen amfani da damar da take da shi da zurfafa hadin gwiwarsu don amfana wa jama'arsu ta hanyar inganta dangantakarsu.
Mr Singh ya bayyana cewa, ziyarar firaminista Li Keqiang tana da babbar ma'ana, wadda za ta sa kaimi ga inganta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin Indiya da Sin. Singh ya amince da ra'ayin Li Keqiang game da dangantakar kasashen biyu da kuma shawararsa game da yadda za a inganta dangantakarsu. Singh yana son yin kokari tare da kasar Sin wajen aiwatar da ayyukan da suka cimma daidaito, da sa kaimi ga samun ci gaban hadin gwiwarsu a dukkan fannoni.
Li Keqiang ya jaddada matsayin gwamnatin kasar Sin kan batun Tibet. Singh ya ce, gwamnatin kasar Indiya tana ganin cewa, yankin Tibet yanki ne na kasar Sin, ba a amince da duk wani irin abin da zai tada yaki da kasar Sin a kasar Indiya ba. (Zainab)